Ana Zargin Wasu Sun Wawure Biliyoyin Nerorin Gwamnatin Tarayya Na Sansanin 'Yan Gudun Hijira

Sanata Shehu Sani (cikin farar riga ) tare da tawagarsa

Kwamitin da Majalisar Dattawa ta kafa na sa ido akan kudaden da gwamnatin Najeriya ke bayarwa domin sansanin 'yan gudun hijira ko IPDs ya ziyarci jihohin Borno da Yobe domin gani da ido da kuma yadda aka kashe kudade kimanin nera biliyan takwas da gwamnatin Najeriya ta bayar.

Shugaban kwamitin Sanata Shehu Sani yace gwamnatin tarayya ta bayar da fiye da nera biliyan takwas domin taimakawa wadanda suke sananin 'yan gudun hijira a jihohin arewa maso gabas da rikicin Boko Haram ya daidaita.

To saidai a zagayawar da kwamitin yayi Sanata Sani yace basu ga abun da aka yi na a zo a gani ba a sansanin 'yan gudun hijiran da dimbin kudaden da gwamnatin tarayya ta bayar da yanzu sun fi nera biliyan takwas.

Muryar Amurka na cikin wadanda suka rufawa kwamitin baya lokacin da tawagar ta ziyarci sansanonin 'yan gudun hijira dake cikin birnin Maiduguri.

Sanata Shehu Sani yayi karin haske akan abun da suka gano.Yace gwamnatin tarayya ta turo biliyoyin nerori amma babu yadda za'a ga kudin a wuraren da suka kai ziyara. Yace asibiti an ce wai sojoji ne suka kafa suke kuma kula dashi. Makaranta Majalisar Dinkin Duniya take yi. Kungiyoyi suke taimakawa da abinci, inji Sanata Sani. Ya tambaya yace ina kudin da gwamnatin tarayya ta aiko suke tafiya.

Kudin ba ma na gine-gine ba ne, kudi ne na a taimakawa 'yan gudun hijira acewar Sani. Shehu Sani yace wadansu mutane suna anfani da 'yan gudun hijiran suna tara ma kansu dukiya a Abuja..Injishi wasu ma basu taba zuwa yankin arewa maso gabas ba.

Shehu Sani yace mako mai zuwa zasu gayyaci mutane da zara sun koma Abuja. Yace duk wanda suka kama ya saci kudi zasu sa a gurfanar dashi a gaban kotu.

Shi ma Sanata Malam Ali Wakili dake cikin tawagar yace da mutum ya je sansanin zai ga mutane suna cikin wani hali mai ban tausayi musamman yadda mata da yara da iyalansu suke, da yadda suke kokarin ciyar da kansu ko saman ma kansu tufafi. Yara basa zuwa makaranta mai kyau haka inda suke kwanciya tamkar na dabbobi ne. Yace wasu kungiyoyi ma sun mayar da 'yan gudun hijiran saniyar tatsa, sun zama abun samun kudi.

'Yan gudun hijiran sun tabbatar ba'a basu abinci isasshe balantana ma samun kula mai kyau.

Ga rahoton rahoton Haruna Dauda Biyu da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Zargin Wasu Sun Wawure Biliyoyin Gwamnatin Tarayya Na Sansanin 'Yan Gudun Hijira - 3' 58"