A hirar shi da manema labarai, Malam Arma, malamin Mustapha almajirin da aka kwakulewa ido ya bayyana cewa, ranar lahadi suna karatu wadansu mutane suka kawo yaron a kan babur su ka ce sun ganshi ne a kwance, kuma sun lura an yi mashi rauni kamar an kwakule mashi idanu.
Malamin ya bayyana cewa, bayan wadanda suka kawo almajirin sun tafi sai ya dauke shi zuwa wajen mai unguwa daga nan kuma suka nufi ofishin ‘yan sanda. Yace bayan da aka tura shi ofishin ‘yan sanda da lamarin ya faru, nan da nan ‘yan sanda da masu aikin tsaro ‘yan sa kai su ka fita domin taimakawa da kuma gudanar da bincike.
A nashi bayanin, kawun yaron da aka kwakulewa idon ya nuna gamsuwa da yadda ‘yan sanda da jama’a su ka dauki batun da muhimmanci da ya kai ga kama matashin da ya kwakule wa almajirin ido, ya kuma yi kira ga ‘yan sanda su yi wa yaron adalci.
Da ya ke bayyana yadda lamarin ya faru, Isa Hassan, matashin dan shekaru 17 da ake zargi da kwakulewa almajirin idon ya bayyana cewa, abokin shi, jikan tsohuwar ne ya shaida mashi cewa, kakarshi na bada maganin bata, shi ne ya je domin neman taimako a kokarin gujewa bacin rana idan su ka yi karo da ‘yan fashi da ya ce suna yi masu barazana a daji lokacin da su ke neman itace domin gudanar da sana’ar su ta ‘yan gawayi.
Bisa ga bayaninsa, tsohuwar ta ce yin maganin bata yana da wahala dalili ke nan da masu kudi kawai su ke iya yin shi. Ya ce, tsohuwar ta gaya mashi cewa, ana bukatar idon mutum domin hada maganin, sai dai ta ce, samun idon yana da wuya domin ko mutum yana da dubu biyu ba zai iya sayen idon ba. Sai dai ta ce, idan zai iya samun idon ya kawo mata zata hada mashi layar batar.
Matashin Isa Hassan ya bayyana cewa, da ya fita daga gidan tsohuwar sai ya ga almajirin a kan titin uguwarsu ya kira shi ya yaudare shi da cewa zai sa shi aiki ya biya shi. Bayan yaron ya bi shi suka tsallaka titi sai ya kada shi ya daure mashi hannuwa ta baya ya kwakule mashi ido ya barshi a wurin.
tsawon-kwanakin-da-aka-yi-garkuwa-da-hanifa-kafin-tuntubar-iyayenta
dalilin-da-ya-sa-na-kashe-hanifa-abdulmalik-tanko
an-gurfanar-da-wadanda-ake-tuhuma-da-kashe-hanifa-a-kotu
Bisa ga bayanin matashin, da ya kaiwa tsohuwar sai ta ce ya rike idon tukuna sai ya kai mata Naira dari biyar ta yi Kadin makauniya. Wannan ya sa ya tafi da idon gida ya je ya daure a tsumma ya sa a ruwa kafin ya tafi neman aikin da zai hada kudin. Yace bayan ya yi aikin kwana hudu ya sami kudin sai ya je ya dauki idon domin ya kaiwa tsohuwar amma ya tarar idon ya narke ya zama ruwa sai ya zubar da ruwan baki daya.
Matashin ya bayyana cewa, da farko ba maganin bata ya je nema ba, yaje neman maganin tsari ne daga baya ne ya nemi a hada mashi maganin batan.
A nashi bayanin, yaron da aka kwakulewa idon ya bayyana cewa, matashin ya kira shi ne ya ce zai sa shi aiki ya biya shi da abinci, amma ya kai shi jeji ya kwakule mashi ido ya bar shi a wurin inda ya kwana kafin wadansu su ka gan shi su ka kai shi wurin malamin shi.
Jikan tsohuwar, Sani Abdulraham dan shekaru 16 ya bayyana cewa, matashin da ake zargi da kwakulewa almajirin ido ya je wurinshi ne ya tambaye shi inda zai iya samun layar bata, shi kuwa da yake ya san kakar tana bada maganin gargajiya sai ya shawarce shi ya je wurinta mai yiwuwa ya samu.
Tsohuwar da ake zargi da sanadin kwakule idon almajirin, Sayyada Furera ta bayyana cewa, an yi mata aure tana da shekaru bakwai da haihuwa, ta kuma tabbatar da cewa, shekarun ta dari. Sai dai ta ce ita ainihi unguwar zoma ce, tana kuma sana’ar Kadin auduga. Tace matashin makwabcinsu ne kuma abokin jikokin ta ne.
Bisa ga bayanin ta, tana bada maganin gargajiya na kananan cututuka sai dai ta musanta wata masaniya game da dalilin kwakulewa yaron ido.
Ku Duba Wannan Ma Hanifa: Abinda Mai Yiwuwa Ba Ku Sani Ba Daga Bakin MahaifiyartaA bayaninsa, kakakin rundunar ‘yan sanda Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun sami labarin kwakulewa yaron ido ne ranar 20 ga watan nan na Maris suka sami labarin, kuma nan da nan kwamishinan ‘yan sanda na jihar Sama’ila Shu’aibu ya bada umarnin kamo duk wadanda su ke da hannu a wannan aika-aikar aka kuma yi nasarar kama yaron tare da taimakon ‘yan unguwar.
Bisa ga cewar Kakakin rundunar ‘yan sandan, yaron ya amsa laifin ya kuma yi masu bayani dalla dalla yadda lamarin ya faru da kuma dalilin shi na kwakule wa yaron ido. Ya kuma ce an maida batun ofishin binciken miyagun laifuka kuma da zarar an kamala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a kwakulewar yaron idon gaban kotu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake cin zarafin kananan yara a jihar kano ba. Ko bayan garkuwa da Hanifa wata yarinya ‘yar shekaru biyar da ake zargin malaminta da garkuwa da ita da ya zama ajalinta, ‘yan sanda sun kama mutane da dama a lokuta dabam bisa laifin cin zarafin kananan yara da ya hada da kashe ‘ya’yanta da wata ma’aikaciyar jinya ta yi , wadda ta yi amfani da adda ta kashe ‘ya’yanta biyu ‘yan shekaru 6 da kuma uku kafin ta gudu daga gidan. Da kuma rahoton kashe wani yaro mai suna Musa Salihu a Narayi da ‘yan sanda su ka tabbatar daga jerin cin zarafin kananan yara da ake fuskanta a jihar.
Ku Duba Wannan Ma Babu Wanda Ya Illata Jikin Hanifa-AbdulmalikSaurari cikakken bayanan cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5