Lamarin ya faru me a ranar 27 ga Nuwamba inda masu zanga-zanga suka datsewa ayarin motocin sojan Faransa hanya lokacin da suke shirin zuwa garin Gao na kasar Mali.
A washegarin tarzomar ta yi sanadin mutuwar mutane 2 a garin Tera wanda ya sa wasu ‘yan Majalisar Dokoki suka shigar da takarda a gaban shugaban Majalisa akan bukatar Ministan tsaron kasa Alkassoum Indatou da takwaransa na cikin gida Hamma Souley su bayyana a zauren Majalisar domin su yi bayani akan wannan al’amari. To sai dai har yanzu haka ba ta cimma ruwa ba.
Wannan ya sa aka fara zargin kakakin Majalisar Seini Oumarou da yunkurin kare Ministocin lamarin da ke nuna taka doka inji wani ‘dan majalisa Alio Namata.
Rashin zuwan wadanan Ministoci ya haifar da mahawara a zauren Majalsar dokoki kafin daga bisani kakakin Majalisar ya saka ranar tattauna wannan batu na kisan matasan garin Tera.
Ya ce an dan sami kuskure da rashin fahimta a tsakanin sakatarIyar Majalisar Dokokin kasa da kwamitin shugabancin Majalisar a wannan rana, mafari kenan da ba a sanar da ‘yan Majalisar cewa Ministan tsaron kasa da takwaransa na cikin gida sun yi tafiya saboda haka a dau hakuri a dakata gaba amma kuma za su yi kiran su domin su zo su yi bayani a ranar 23 ga watan Disamba.
Rashin halartar Ministan tsaron kasa da takwaransa na cikin gida a zauren Majalisar ya yi matukar ja mata suka a ‘yan kwanakin nan a kafafen sada zumunta inda wasu ‘yan kasa ke ganin gazawar Majalisar wajen tilastawa mambobin gwamnati zuwa su yi aikin da kundin tsarin mulkin kasa ya wajabta masu, yayin da wasu kuma ke ganin rashin samun dama ne ya hana Ministocin hallara a zauren Majalisar saboda wasu ayyukan da suka sha gabansu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5