ADAMAWA, NIGERIA - Yayin tattaunawa da wani abokin daya daga cikin wandanda suka mutu a lokacin hadarin, ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da abin da jami’an kwastam din suka yi har ya yi sanadiyar rasuwar abokin na su.
Wani da ya shaida lamarin da ya bukaci da a sakaya sunansa, ya ce motar kwastim din ta taso ne a guje daga karamar hukamar Girei, suna bin wani mai karamar mota kirar Sitalet wanda har suka shigo yankin na Hayingada inda aka buge mutane da dama, hudu daga cinkinsu suka mutu.
Al’ummar mazauna yankin karamar hukamar Girei sun koka kan yadda ‘yan kwastam din suka dade suna janyo irin wanna hadari, amma hukumar ta yi ko in kula akan alamarin in ji wani dan karamar hukamar Girei da ya bukaci da a sakaya sunansa saboda tsaro.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa SP Sulaiman Yaya Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce yanzu haka tuni jami’ansu suka fara gudanar da binchike a kan al’amarin.
Saurari cikakken rahoto daga Lado Salisu Garba:
Your browser doesn’t support HTML5