Kamar yadda Mr. Dikko ya bayanna, nan gaba mutane baza su yi mu’amala da jami’an kwastom ba ido da ido, sai ta na’u’ra mai kwakwalwa.
Mr. Dikko ya kara da cewa hulda ido da ido kan kawo cin hanci da rashawa, shiyasa suke ganin yin amfani da na’u’ra zai martaba hukumar.
Bisa yadda fasalin ya tsara, ‘yan kasuwa suma zasu shafu daga wannan sauyi, saboda ana bukatar su aika da sako ta na’u'ra zuwa ga hukumar Kwastom, kafi su shigar da kaya Najeriya.