Ana Zargin Houthi Da Kai Hare Hare Kan Jiragen Ruwan Fatauci-Martani Ga Zub Da Jini A Gaza

  • VOA

Jiragen ruwa yakin Iran

A yau Asabar harin wani jirgin mara matuki a yammacin gabar tekun Indiya ya afkawa wani jirgin ruwan fatauci mai alaka da Isra'ila, a cewar Ambrey, wani kamfanin tsaron teku na Burtaniya.

Ambrey ya ce gobara ta tashi a cikin jirgin ruwan dakon man da ke dauke da kayan sanadari wanda yake dauke da tutar kasar Laberiya, da ya taso daga Saudiyya zuwa Indiya.

Wani jami'in sojin ruwan Indiya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ya amsa wata kirar bukatar taimako da safiyar Asabar.

Jami'in ya ce "An tabbatar da lafiyar ma'aikatan jirgin da kuma na jirgin, haka kuma sojojin ruwa sun aike da wani jirgin ruwan yaki domin isa yankin da kuma bayar da taimako kamar yadda ake bukata," in ji jami'in, wanda ya ki bayyana sunansa tun da ba shi da izinin magana kan lamarin.

An yi ta samun hare-hare da makamai masu linzami da na jirage mara mtuka daga 'yan kungiyar Houthi da ke samun goyon bayan Iran kan jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya tun bayan harin ta'addancin da Hamas ta kai kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba. Houthis dai ta ce tana goyon bayan Falasdinawa.

Hare-haren sun sa wasu kamfanoni suna zagaye da jiragen ruwansu ta yankin kudancin Afirka, hanya mai tsawo da tsada.

Sai dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin lamarin na yau Asabar.