Ana Yi Mana Kallon Ba Dai-Dai Ba

Hadiza Ado Jinta

Jama’a suna daukar dabi’ar wasan kwaikwayo a matsayin halayyar masu gabatar da wasani na zahiri inji Hadiza Ado Jinta wata mai shirin wasan kwaikwayi a Radiyo.

Ta furtahaka ne a hirarsu da wakiliyar Dandalinvoa Baraka Bashir, a birnin Kano,tana mai cewa sha’awace ta kaita ga batun wasan kwaikwayo.

Ta ce daga sama ta fara harkar wasan kwaikwayo kuma ta fara a shekara ta 2005, inda ake gayyartarsu batare da wasan yana rubuce ba sai dai a ce ‘Hadiza ke ce wancen ana son kiyi dabi’a kaza,

Daga bisani sai ta fara samun wasan kwaikwayon da za’a basu a rubuce sai dai idan da halin suyi kwaskwarima ko wani kari domin yayi armashi.

Hadiza Jinta ta ce baya ga sha’awa tana kuma fadakar da masu sauraro, sannan tana nishadantarwa. Ta ce wasan kwaikwayon ‘Idan rana ta fito’ ne wasan da ya fito da ita aka santa.

Ta ce babban burinta shine ta zauna ta rubuta labari da kanta inda wasu zasu karanta su kuma fadakar da jama’a akai.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana YI Mana Kallon Ba Daidai Ba 4'14"