An gurfanar da sojoji 13 daga cikin wadanda ake zargi gaban kotun, baki ‘dayansu sanye da kayan soja, domin su saurari laifukan da ake tuhumarsu da su, wanda suka hada da kisan kai da fyade da gallazawa da kuma satar kayayyaki lokacin da aka kai harin a watan Yulin da ya gabata kan wani Otel a babban birnin Sudan ta Kudu. Babban lauyan sojoji mai gabatar da ‘kara ya ce duk wanda aka samu laifi zai iya fuskantar hukuncin kisa.
An dai fara shari’ar ne a sansanin soja na Giada dake a birnin Juba. Hudu daga cikin wadanda ake zarga suna sanye da kayan sojojin dake gadin shugaban ‘kasa ne.
Mai gabatar da ‘kara, Kanal Abubakar Moahmmed Ramdhan, ya nemin manajan Otel din da aka kai harin ya bayyana abin da ya faru ranar 11 ga watan Yuli. Michael Woodward, ya ce sojoji 50 zuwa 100 cikin motoci irin na yaki suka karya kofar shiga Otel din suka shiga, bayan da suka fi karfin masu tsaron Otel din.