Ana Tuhumar Matashin Da Ya Harbe Mutum Biyu a Kenosha Da Laifin Kisan Ganganci

Ana tuhumar matashi dan shekara 17 da lafin harbi da kisan ganganci, sabili da harbi da kuma kashe mutane biyu ya yin zanga zangar da ake gudanarwa dare uku a jere a Kenosha na jihar Wisconsin, biyo bayan harbe bakar fata da ‘yan sanda suka yi ranar Lahadi.

Bayanan da aka kafa a shafin yanar gizo na kotu, ya nuna an kama wanda ake zargi a gidansu da ke Antioch a jihar Ilinois. Saboda mai laifin mai karancin shekaru ne ya sa kwamandan ‘yan sandan Antioch Norman Johnson ya ki bayyana sunan sa. Nan da nan yan sanda ba su ba da karin bayani a kansa ba.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya wallafa a shafinsa na Twitter a jiya Laraba cewa, zai aika da jami’an tsaron gwamnatin tarayya don maido doka da oda a Kenosha.

A wani hoton bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter, tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Democrat a zaben uku ga watan Nuwamba, ya ce ya yi magana da iyalan Blake kuma ya gaya musu za a tabbatar da bi musu hakkinsu.