Taron da ke hangen hada kan al’umomin yankin AES tare da ba su goyon baya a gwagwarmayar da kasashen suka kaddamar da zimmar kwatar cikakken ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Shugaban jam’iyyar Incin Afrika Abdorhamane Oumarouna ya ce ya na tsamanin birnin Yamai na iya shirya irin wannan haduwa ta kasa da kasa don yin Allah-wadai da akidar mulkin mallaka, wanda ya ce bai ta ba tunani ko a mafarkin shugabaninmu za su jagoranci ko su halarci taron yaki da manufofin ‘yan mulkin mallaka ba.
Taron na da manufar farfado da yunkurin dadedden burin nan na dunkulewar nahiyar Afrika amma a karkashin turbar cikakken ‘yancin kai.
Shugaban Sakatariyar jam’iyyar Panafricanism Today Nely Rozeto na wakiltar Afirka ta Kudu a wannan haduwa, yace a ranar 15 ga watan nan na Nuwamba sun yi buki cikin yanayin bacin rai don tunawa da zagayowar ranar cika shekaru 114 da kasashen mulkin mallaka suka hadu a Turai da kuma taron Berlin na 1894 a ci gaba da karkasa arzikin Afrika da al’umominta domin kansu.
Yau shekaru 114 bayan haka mun hadu a nan Yamai domin hada kai da Mali, Burkina Faso da Nijar.
Taron wanda ke kammala a wannan Alhamis 21 ga watan Nuwamba zai fitar da sanarwar da aka ayyana a matsayin sanarwar zaman birnin Yamai.
Wannan yunkuri na lalubo hanyoyin ceto Afrika daga kangin mulkin mallaka na wakana a wani lokacin da rikicin siyasa ya kunno kai a Mali inda sabanin ra’ayi tsakanin sojojin da ke mulki da firaiministan Choguel ya yi sanadin tsige shi daga mukaminsa tare da rusa majalisar ministocinsa.
Tuni aka maye gurbinsa da tsohon ministan ci gaban karkara Kanal Abdoulaye Maiga.
Tsohon firaiministan na zargin Janar Assimi Goita da mukarrabansa da yin gaban kansu wajen jan ragamar mulki a wani lokacin da ya kamata su shirya zaben dimokradiya kamar yadda aka yi alkawari a shekarar 2022.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5