Ana Taron Kasa da Kasa Akan Fahimtar Harkokin Addini Da Siyasa a Kano

Sarkin Kano Muhammad Lamido Sanusi wanda ya bude taron

Jiya a Kano aka fara taron kasa da kasa na yini biyu akan koyarwa da fahimtar harkokin addini da siyasa na marigayi Dr Hassan AL-Turabi, wanda a shekarun baya-bayan nan ya jagoranci kawo sauyi kan lamuran addini da siyasa a kasar Sudan da sauran sassan duniya.

Gidauniyar kula da harkokin ilimi ta AAFAAQ dake Kaduna hadin gwiwa da cibiyar wayar da kan musulmi da wanzar da fahimta tsakanin addinai da takwararta cibiyar nazarin jinsin dan Adam, dukkanin su a Jami’ar Bayero Kano sune suka shirya taron dake gudana a harabar Jami’ar ta Bayero.

Farfesa Ibrahim Na’iya Sada dake zaman shugaban kwamitin tsare-tsare ya fayyace dalilan shirya taron.

A cewarsa sun gayyaci mutane dake da sha’awa na ilimi a tsarin musulunci saboda musulunci addini ne na rayuwar dan Adam na koyaushe na kuma kowane zamani, har abada kuma. Idan ilimi ya yawaita mutane ba zasu kyamaci juna ba ko kuma wani. Ilimin musulunci ban a kyamar wani ba ne. Ilimi ne da ya tsaya kan kare hakkin dan Adam, da musulmi da wanda ma ba musulmi ba.

Wakilai daga Kasashen Afrika 8 ne da kuma Burtaniya ke halartar taron wadanda suka hada Sudan Ghana da Sanagal, Masar , Mauritania Nijar, Qatar da kuma mai masaukin baki Najeriya.

Injiniya Sa’id Mukhtar Abubakar na daga cikin mahalarta daga Ghana.

Y ace ilimin da al-Turabi ya fitar, kokari ne na samar ma jama’a mafita domin a samu zamantakewa mai kyau. Rubuce rubucensa suna jawo hankalin malamai su samar ma mutane mafita daga matsalolin yau da kullum.

Ustaz Harun Ahmad Bubakar daga Jamhuriyar Nijar na daga cikin daliban marigayi Dr Hassan Al-Turabi. Y ace irin horaswar da suka samu ya sa suka zauna lafiya duk da cewa sun fito ne daga wurare daban daban.

Jimlar makaloli 19 ne shehunnan malamai zasu gabatar akan batutuwa daban daban bisa mahanga da fahimtar marigayi Dr Hassan al Turabi wadanda suka hada da shigar da mata cikin harkokin siyasa, lamuran shari’a da ilimi da zamantakewa da dai sauransu.

Taron wanda za’a kammala a Talatar nan, sarkin Kano Malam Muhammadu Sanudi ne ya jagoranci bude shi, inda ya yi bitar gwagwarmayar yada ilimin addinin musulunci dai-dai da zamani na Dr Hassan Al-Turabi wanda ya rasu a shekara ta 2016 yana da shekaru 84 a duniya.

A saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Taron Kasa da Kasa Akan Fahimtar Harkokin Addini Da Siyasa a Kano – 3’ 33”