BAL: Rwanda Ta Lallasa Najeriya Da Ci 83-60

Wasan Rivers Hoopers na Najeriya da Patriots na Rwanda, ranar 16 ga watan Mayu, 2021

Rwanda na rukuni daya ne da Madagascar, Najeriya da Tunisia. Yanzu ita ce ke gaba a saman teburin rukuninsu na A.

'Yan wasan Patriots of Rwanda, sun lallasa takwarorinsu na Najeriya Rivers Hoopers da ci 83-60 a gasar zakarun kwallon kwandon nahiyar Afirka ta BAL.

Wannan shi ne wasan farko da aka bude gasar da shi, wacce ake yi a Kigali babban birnin Rwandan.

A bangaren 'yan wasan Rwanda, an ga mawakin zamani Jermaine Cole yana bugawa Patriots - har ma ya ci kwallo mai maki uku.

Rwanda na rukuni daya ne da Madagascar, Najeriya da Tunisia. Yanzu ita ce ke gaba a saman teburin rukuninsu A.

Wannan gasa ita ce ta farko da aka fara wacce aka kaddamar da ranar Lahadi 16 ga watan Mayun, za kuma kammala ta ne a ranar 30 ga watan na Mayu.

An kirkiri wannan gasa ce da hadin gwiwar hukumar kwallon Kwandon Amurka ta NBA da kuma ta kwallon Kwando ta duniya.

Kungiyoyi 12 daga nahiyar Afirka suka shiga wannan gasa, wadanda suka hada da, Algeria, Angola, Kamaru, Masar, Madagascar, Mali, Morocco, Mozambique, Najeriya, Rwanda, Senegal da kuma Tunisia.

Wannan shi ne karon farko da hukumar NBA ta kaddamar da wata gasa a wajen yankin arewacin Amurka. Ga jerin sunayen kungiyoyin da zakarun ‘yan wasansu da suka fi fice.