Ministan Man fetur Timipre Sylva, ya yi bayani cewa dokar da gwamnati ta kai Majalisar Dokoki ba wacce za ta shafe kamfanin NNPC ba ce, face wacce za ta sauya shi zuwa Kamfani mai cin gashin kansa a bisa sharudan sauye sauye da aka aiwatar kan dukan rassan man fetur a kasar.
To saidai wanan mataki ya sa kwararu da masu ruwa da tsaki tafka mahawara akan amfanin da wannan sauyi zai kawo wa kasar.
Kwararre a fanin tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati, ya bayyana cewa matakin yana nuna an cire tallafi akan man Fetur da ake sayarwa a kasar, wanda zai ba kamfanin damar cin gashin kansa kuma yana ganin yin haka zai ba kasar sararin samun kudaden shiga masu yawan gaske a sanadiyar zuba jari a wannan bangaren.
Amma ga tsohon mukadashin shugaban kungiyar Ma'aikatan Man fetur ta kasa Komred Isah Tijjani, na cewa mayar da Hukumar NNPC kamfani ba wani abu ne sabo ba, kuma ba zai sauya komi ba, wannan mataki ne kawai da gwamnati ta yi amfani da hurumin ta don kasuwar Man Fetur ta yi halin ta.
Amma ga mataimakin shugaban kungiyar dillalan Man Fetur ta kasa IPMAN Abubakar Maigandi Dakingari, cewa ya yi yana goyon bayan wanan mataki domin zai ba yan kasuwa na cikin kasar damar cudanya da yan uwansu na kasashen waje da za su zuba hanun jari a kamfanin.
A yanzu dai Majalisar Dattawa ta yi wa dokar karatu na farko a wani mataki na kafa tarihi da tabbatar da dokar a cikin karamin lokaci kamar yadda shugaban Majalisar Ahmed Lawan ya fada a lokacin wani zama da suka yi.
Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.