Hukumar da ke yaki da cuta mai karya garkuwar jikin dan'adam a kakashin Majalisar Dinkin Duniya, ta ce ana kara samun hanyoyin kai wa ga magunguna.
WASHINGTON D.C —
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, ana samun gagarumar nasara wajen yaki da kwayar cutar HIV da ke hadda cutar AIDS mai karya garkuwar jiki.
Rahoton na baya-baya nan, an fitar da shi ne yayin da ake shirye-shiryen bikin tunawa da ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yin dubi kan cutar. Dr Anthony Fauci na daya daga cikin likitocin da ke fafatukar neman makarin kwayar cutar ta HIV.
Rahoton ya kuma kara da cewa akalla mutane miliyan 21 da ke fama da cutar ne ke karbar magani, wanda hakan adadi ne da ya haura rabin mutanen da ke dauke da cutar.
Burin majalisar Dinkin Duniya shi ne a kawo karshen annobar nan da karshen shekarar 2030.