Kasashen sun sake jaddada kudurinsu na cetowa da farfado da wannan tabkin da a yanzu fadinsa bai kai kashi 10 cikin 100 na yadda yake shekaru 50 da suka shige ba.
WASHINGTON, DC —
Kasashen dake cin moriyar Tabkin Chadi, sun sake nanata kudurinsu na farfado da tabkin, wanda ruwansa a yanzu bai kai ko kashi 10 cikin 100 na yadda yake shekaru 50 da suka shige ba.
Sauyin yanayi da rashin kulawa, sune manyan dalilan da suka sa tabkin na Chadi, wanda mutane fiye da miliyan 30 suka dogara kansa don noma da kamun kifi da kuma ruwan sha, yake kafewa.
Wakilan kasashen da suka hadu suka kafa Hukumar Raya Tabkin Chadi mai hedkwata a birnin N'Djamena a kasar Chadi, sun hallara a Abuja domin rattaba hannu a kan yarjejeniyar samar da kudaden farfado da wannan tabki,
'Yan majalisun kasashen biyar, sune suka sanya hannu kan yarjejeniyar a wannan taro na Abuja.
Kakakin majalisar dokokin jamhuriyar Nijar, Hamma Ahmadou, yace saio an nemi hadin kan wasu kasashen dabam ma wadanda wannan aikin zai shafi yanayin kasashensu, kamar Kwango Brazzaville, Kwango Kinshasa da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sannan a samo hanyar da za a iya samun kudaden gudanar da ayyukan sake farfado da tabkin.
Yace kudin da za a bukata domin gudanar da aikin yana da yawa, amma muddin ba a yi hakan ba, to Tabkin na Chadi zai kone baki dayansa ya zamo tarihi kawai.
Shugaban Hukumar Raya Tabkin Chadi, Sunusi Imrana Abdullahi, yace sun gano yadda za a iya farfado da wannan tabki, amma abin zai dauki lokaci, amma a yanzu su na da kwarin guiwa a kan cewa haka zata cimma ruwa.
Ga rahoton Nasiru Adamu Elhikaya daga Abuja

Your browser doesn’t support HTML5