Alkalan shara’a a Jamhuriyar Nijar, sun bayyana damuwa, da yadda suka ce gwamnatin kasar ke take dokoki, da ka’idojin gudanar da mashara’antu.
Wannan shi ne dalilin da kungiyar alkalan shari'ar ta ce ba za ta yadda da shi ba, saboda haka ta gargadi mahukunta su koma kan hanyar gaskiya, sai dai Ministan shari’ar kasar ya musanta wannan zargi.
Nade-nade, da canje-canjen wuraren aikin da aka yi wa alkalan shari’a a lokacin taron majalisar koli mai kula da sha’anin shari’a, wato "Conseil Superieur de la Magistrature," na bayan nan da ya gudana a karkashin jagorancin shugaban kasar Nijar, na daga cikin dalilan da ke zama mafarin sabuwar takaddama tsakanin alkalan shari’a da gwamnati, kamar yadda kungiyar alkalai ta SAMAN ta bayyana a wata sanarwar da ta fitar.
Da yake mayar da martani, Ministan shari’a Marou Amadou, ya ce babu kamshin gaskiya akan dukkan zarge-zargen alkalan.
kungiyar alkalan shari’a ta SAMAN ta sanar da cewa za ta dauki matakan da suka dace muddin hukumomin kasar Nijar suka yi watsi da wadannan korafe-korafe na ‘ya'yanta.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5