Wannan fasahar za ta ba jama’a damar yin bindigogi daga cikin gidajensu.
Babban Atoni-Janar din Washington, Bob Ferguson ne ke jagorantar kai karar, ya ce yana da tambaya ga gwamnatin Trump.
“me ya sa gwamnatin ke ba masu manyan laifuffuka damar samun makamai a saukake? Wadannan bindigogin da za a iya sarrfa da na’urar kwamfuta ba su da rijistar, kuma suna da wahalar tantancewa ko da an yi amfani da na’urar gano karfe, sannan kuma kowa na iya samun bindigar komai karancin shekarun su, ko da ba a duba lafiyar kwakwalwarsu ba, ko kuma tarihin laifuffukan da suka aikata.
Shugaba Trump ya fada a shafin sa na twitter cewa, yana duba wannan batun.
Zanen bindigar da wani kamfanin Texas yayi ya ba duk wani mai na’urar buga takarda ta 3D damar sarrafa wasu bangarorin bindigar ta roba da kayan hada ta ba su wuce ‘yan daruruwan daloli ba.