Ana Nazarin Yiwuwar Sake Bude Makarantu A Najeriya

'Yan makaranta.

Yayin da ake haramar bude makarantu a Najeriya, hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasar NCDC, ta gana da masu ruwa da tsaki don sanin shirin da aka yi, yayin da a nata bangaren Kungiyar Malamai ke nuna damuwarta kan wannan batu.

Dalibai a Najeriya sun shafe fiye da watanni uku suna zaune a gida sanadiyar annobar coronavirus.

Ya zuwa yanzu gwamnatocin jihohi suma sun bi sahu wajen haramar sake bude makarantu, bayan shafe watanni dalibai na gida.

Ibrahim Hamman Adama Tukur, shi ne shugaban makarantar sakandare ta Aliyu Mustapha da ke Yola babban birnin jihar Adamawa, ya kuma bayyana irin damarar da makarantu suka yin ta gani dalibai sun koma aji.

Ya ce gwamnati jiha ce ta basu damar bude makarantu bisa wasu ka’idodi da za'a kaucewa kamuwa da cutar COVID-19.

Ya kara da cewa ya gana da dalibai, inda kuma ya gargadesu da su nisanta da juna na akalla mita biyu, haka zalika ya ce ya gana malaman makarantar a kan yanda zasu yi aikin ba tare da jefa daliabn cikin hadarin kamuwa da cutar ba.

To sai dai kuma yayin da iyaye da dalibai ke murnar sake bude makarantun, hadakar kungiyar malamai a Najeriya ta NUT, ta ce ba nan gizo ke saka ba, domin kafin bude makarantun akwai matakan da ya kamata gwamnatocin jihohi su dauka game da abin da ya shafi malaman da suma ka iya fadawa hadarin kamuwa da cutar ta coronavirus.

Shugaban kungiyar malamai ta NUT a jihar Adamawa, Kwamared Rodney Nathan, ya ce suna maraba da wannan mataki, to amma kuma da sauran rina a kaba.

Ya ce "ya kamata a yi la’akari da girman azuzuwa da adadin daliban da suke zama a aji da kuma batun nisanta da juna. In kuwa ba a iya magance wannan batutuwa ba, to ci gaba da rufe makarantun shine mafi katari."

Tun farko sai da hukumar kula da yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC, ta gana da masu ruwa da tsaki game da matakan da ya kamata a dauka kafin sake bude makarantun.

Dr. Fahat Muhammad na hukumar ta NCDC, a taron masu ruwa da tsaki a Yola, ya musanta batun cewa su ne basa son a bude makarantu.

Ga dai rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola:

Your browser doesn’t support HTML5

ANA NAZARIN YIWUWAR SAKE BUDE MAKARANTU A NAJERIYA