Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Bude Makarantu Ranar 12 Ga Watan Oktoba


Yara a wata makarantar Firaimare
Yara a wata makarantar Firaimare

Hukumomi a Najeriya sun ayyana 12 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a bude makarantu a duk fadin kasar bayan da aka kwashe sama da wata shida makarantun na kulle sanadiyyar annobar COVID-19.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya sanar da umurnin bude makarantun yayin wani taron manema labarai da ya kira a ranar Juma’a inda ya bayyana cewa za a bude daukacin makarantun hadin kai na "Unity Schools" a wannan rana.

Ma’aikatar ilimin kasar ta ce ta dauki wannan matakin ne, bayan da ta nemi shawarar kwamitin da shugaban kasa ya kafa don yaki da annobar ta COVID-19.

Adamu ya kuma kara da cewa, za a tabbatar da cewa makarantun sun bi ka’idojin da gwamnati ta gindaya domin kare lafiyar dalibai da malamai.

Kafafen yada labarai da dama sun ruwaito Ministan yana cewa, makarantun jihohi da na masu zaman kansu, su kintayi lokacin da ya fi musu don bude nasu makarantun.

Najeriya na da makarantun hadin kai na Unity 104.

Mallam Adamu ya kuma yi gargadin cewa gwamnati za ta rufe duk makarantar da aka samu da laifin bijirewa ka’idojin da gwamnati ta gindaya musamman idan aka samu bullar cutar a makarantar.

Mutum 59, 001 aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya, 1,112 sun mutu bisa alkaluman da hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta NCDC ta fitar a ranar Alhamis.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG