A wani faifan bidiyon wanda ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta a farkon makon da ya gabata ne kungiyar ta ayyana dokar tare da barazanar hallaka duk wanda ya fito waje daga ranar 9 zuwa ranar 14 ga wata.
Sai dai bayanan da Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tattaro na nuni da cewa , daga ranar Jumma’ar da ta wuce, 9 ga wata zuwa yau, mutane da yawa basu janye daga harkokinsu na yau da kullum ba a fadin yankin.
A garin Aba na jihar Abia wani mazauni Malam Idris Bashir ya ce kasuwanci bai tsaya ko na kwana guda ba, yayin da sauran al’umma ke ci gaba da tafiyar da ayyukansu kamar yadda aka saba.
Ya ce, “Anan Aba, gaskiya abin da ya shafi wannan dokar bai ta yi tasiri ba saboda su ‘yan kasuwa sun bijire wa dokar, kuma an ci kasuwa ranar Jumma’a, an ci ranar Asabar, haka kuma ranar Lahadi an yi duk abin da ya kamata a yi.”
Kazalika, ayyukkan yau da kullum basu tsaya ba a jihar Anambra, inji wani mazaunin garin Onitsha Alhaji Yusha’u Imam.
“Tun daga lokacin da aka yi sanarwar zaman gida na kwana biyar a makon da ya wuce, daga ranar Jumma’a zuwa yanzu kowa na ci gaba da kasuwancin sa. Maganar zaman gida babu, kuma ba a yi ba. Yau ma Talata an bude kasuwa, kuma kowa na ci gaba da harkokin sa,” inji Alhaji Imam.
Mista Jude Obike a Owerri, babban birnin jihar Imo, ya bayyana cewa harkoki na ci gaba da gudana, koda yake harin da wasu ‘yan bindiga suka kai shelkwatar hukumar zabe da ke birnin a safiyar Litinin ya hana wasu mutane fitowa.
Ya ce, “Mutane sun lallaba sun fito, sai dai harin da aka kai shelkwatar hukumar zabe ya haddasa tsoro da ya sa har wasu suka noke a gida.”
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5