Kamfanin harhada magungunan nan na Pfizer, ya ce gwajin baya bayan nan na rigakafin COVID-19 da ya kirkiro, ya nuna yana da ingancin sama da kashi 90 cikin 100, wanda hakan ya zarce abin da aka zata a baya, wanda hakan kuma ya zama labari mai kyau kan yakin da ake yi da cutar coronavirus.
Shugaban kamfanin Pfizer, Albert Bourla ne tare da kamfanin da ke taimaka ma Pfizer, BioTech, su ka yi wannan shelar ranar Litinin game da mataki na uku wanda shi ne na wajejen karshe, na binciken da su ke yi kan wannan rigakafin na su.
Bayanin nasu na cewa, binciken da ake yi ya nuna cewa, rigakafin na da ingancin fiye da 90 cikin 100, wajen kare wadanda su ka sha, muddun ba su dauke da cutar tun farko.
Babban kwararre kan cututtuka masu yado a Amurka, Dakta Anthony Fauci, ya fadi a wata hira da manema labarai ranar Litinin cewa, wannan sakamakon, a ta bakinsa, “abin mamaki ne.”