Sun bayyana cewa, daukar wannan matakin zai janyo matsalar gaske musamman ga ‘yan kasuwa kasancewa, zamani ya kai wani matsayin da harkokin kasuwanci yafi karfi ta hanyar internet da ake gudanarwa da katunan.
Daya daga cikin wadanda Sashen Hausa ya yi hira da shi ya bayyana cewa, yanzu haka yana da wani bako daga Najeriya wanda ya shiga halin tsaka mai wuya, kasancewa an hana fitar da tsabar kudi, ya kuma shigo Amurka ya rasa yadda zai biya kudin Otel da yake an toshe damar amfani da katin daukar kudin.
Wannan dokar ta kuma shafi dalibai dake karatu a kasashen waje da matafiya, da duk wadanda ke fita kasashen waje domin wadansu dalilai da suka hada da neman jinya.
Sun bada shawarar cewa, ko da za a yi gyara bai kamata a yi kan mai uwa da wani ba. Kamata ya yi a duba a gani wadanda ya kamata wannan dokar ta shafa amma bai kamata a yi dokar da, a maimakon gyara zata jefa al’ummar kasar cikin wani mawuyacin hali ba.
Ga cikakken bayanin
Your browser doesn’t support HTML5