Wani rahoto da aka fitar a baya yace kungiyar Human Rights Watch ta nuna bacin ranta na rashin yin abin da ya dace wajen kare irin wadannan matan da tabbatar da 'yancinsu da kuma tabbatar da sun samun ababen more rayuwar.
Kungiyar ta tattara bayanan a kan lalata da kuma yiwa ‘yan mata 43 fyade, wadanda suke zaune a sansanonin gudun hijira guda bakwai dake Maiduguri a jihar Borno.
An samu irin wannan labari a wani sansanin ‘yan gudun hijira dake jihar Adamawa, inda aka yiwa wata ‘yar gudun hijira dake da tabun hankali fyade, wanda yanzu haka ta samu juna biyu, lamarin da yasa kungiyoyin fafutuka ke cewa dole a gudanar da bincike.
Kwamared Abubakar Abdul Salam dake zama shugaban kungiyar Progressive Mind For Development Initiative, PMDI, yace akwai bukatar a sa ido a kan abubuwan dake faruwa a sansanonin ‘yan gudun hijira a Najeriya.
Wakilinmu Ibrahim Abdulaziz ya tattauna da Imam Abari Garki dake zama jami’in hukumar agajin gaggawa a Najeriya NEMA a cikin wannan rahoto:
Your browser doesn’t support HTML5