An kira mutanen Nijar su hada kawunansu saboda zaman lafiya

Bayan zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Nijar Bukar Sani Zilli na jam'iyyar PNDS mai mulki ya fito ya kira 'yan kasar da su hada kawunansu yanzu da aka kammala zabe.

A firar da Muryar Amurka ta yi da Bukar Sani Zilli na PNDS mai mulki a kasar Nijar yace a zaben zagaye farko an samu wasu kurakurai amma a wannan zagaye na biyu hukumar zabe ta CENI ta kokarta.

Cikin 'yan takara 15 Allah ya zabi Muhammadou Issoufou da Hamma Ahmadou da su fafata tare. Yace mutanen Nijar su lura Allah yana sonsu amma wasu sun koma garin Niamey sun kwanta suna cewa mutane basu fito ba.

Amma a garinsu yace mutane sun fito kuma an yi zabe. Mutane sun fito sun yi zabe don haka babu batun kauracewa zaben kamar yadda 'yan adawa suke yayatawa.

Ikirarin 'yan adawa cewa zasu kada shugaban kasa kamar kasa tasu ce kadai bai tabbata ba. Kasa ba tasu bace su kadai. Suna da 'yancin su gujewa zabe.

Ya kira 'yan Nijar gaba daya Allah ya hada kawunan 'yan kasar domin a samu zaman lafiya. Yace Nijar tasu ce kuma babu wanda zai gyara masu kasa sai su. Kasar bata masu adawa ba ce ba kuma ta masu rinjaye ba ce. Kasa ce ta kowa da ya kasance dan Nijar.

Ga karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

An kira mutanen Nijar su hada kawunansu - 4' 08"