Ana Kara Samun Tankiya A Huldar Ciniki Tsakanin Amurka Da China

Wakilan Amurka da na China a kan ciniki

Kasar China tace zata kakaba Haraji na dala biliyan sittin a kan kayan Amurka, da ake shiga da su kasar ta.

Ta maida martanin jim kadan bayan matakin da shugaba Donald Trump, ya dauka na kara haraji dalar Amurka, biliyan dari biyu a kan kayayyakin kasar ta da ake shiga da su Amurka, tare da karin harajin dalar Amurka biliyan dari uku a kan wasu kayyakin da ake kaiwa China.

A ranar litinin ne Ministan kudin kasar China, yace daga ranar daya ga watan Yuni, sabon tsarin Karin kudaden harajin zai fara aiki, daga kashi 5% zuwa 25%, yana mai cewa, Karin zai shafi kayayyakin Amurka dubu 5,140 wadanda ake shiga da su China.

Hukumomin Beijing sun kara da cewa, daukan wannan matakin, martani ne kan irin yadda Amurka ke “yin gaban kanta da kuma kara kudaden haraji a kan kamfononin kasashen wajen, wadanda ke gogayya da nata”

“Ministan, ya kara da cewa China ba za ta taba mika-wuya ga matsin lambar wata kasar waje ba, domin China tana da karfin da za ta kare kanta da hakkokinta, amma muna fatan zamu samu daidaito da Amurka a nan.