Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya ce goyon bayan kasa da kasa na karuwa kan bukatar a ladabtar da gwamnatin Siriya
WASHINGTON, DC —
Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya ce goyon bayan kasa da kasa na karuwa kan bukatar a ladabtar da gwamnatin Siriya saboda zargin da ake mata na kai harin makaman guba.
Kerry ya yi wannan bayanin ne a yayin wani taron manema labarai a jiya Asabar a birnin Paris, tare da Ministan Harkokin Wajen Faransa Laurent Fabius.
Tun da farko a ranar, Kerry ya gana da Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Turai a Lithuania a wani yinkuri na karfafa goyon baya, a daidai lokacin da Amurka ke duba yiwuwar kai hari kan Siriya.
Bayan taron, Babbar Jami’ar Harkokin Wajen Kungiyar Tarayyar Turai Catherine Ashton ta karanta wani jawabi ga kungiyar inda a ciki ta yi kiran da a mayar da martani dalla-dalla kuma karara game da harin makaman gubar da aka kai a Siriya to amma ba ta ambaci matakan soji kai tsaye ba.
Ashton ta kuma ce kungiyar ta EU na son Majalisar Dinkin Duniya ta warware rikicin na Siriya. Ta ce duk wani matakin da za a dauka nan gaba kan Siriya, dole ne ya biyo bayan gabatar da rahoton tawagar binciken Majalisar Dinkin Duniya.
A birnin Paris, Kerry ya ce Shugabannin kasashen Turai sun yi maganganu masu karfi ko da yake har yanzu wasu kasashen ba su amince da daukar matakin soji ba.
Ya kuma ce Shugaba Barack Obama bai yanke shawarar jaran rahoton tawagar binciken Majalisar Dinkin Duniya ba.
A halin da ake ciki kuma, Mr Obama, a jawabinsa na sati-sati da akan yada ta kafar rediyo, kasa mai da martani kan abin da ya kira, “harin fitar hankali da aka kai a Siriya,” zai yawaita kasadar karuwar hare-haren makaman guba nan gaba.
A jawabin da aka yada jiya Asabar, Mr Obama ya ce harin makaman gubar da ake zargin gwamnatin Siriya da kai wa “wani hari ne kai tsaye kan mutuncin bil’adama” da kuma barazana ga tsaron kasa.