Bayanai sun yi nuni da cewa an tsinci gawar Carter ne a gidansa da ke kudancin jihar California.
Washington D.C. —
Rahotanni a Amurka na cewa mawaki Aaron Carter da ya yi fice a fagen waka tun yana matashi, ya rasu. Shekarunsa 34.
Bayanai sun yi nuni da cewa an tsinci gawar Carter ne a gidansa da ke kudancin jihar California.
A karshen makon nan wakilan iyalan mamacin suka tabbatar da mutuwarsa, sai dai ba su yi karin haske kan musabbabin mutuwarsa ba.
Ofishin jami’an tsaron yankin ya ce an kira shi cikin gaggawa da ya kai dauki a wani gida da ke Lancaster bayan da aka tsinci wani mutum a mace.
Aaron Carter, kani ne ga Nick Carter na kungiyar mawakan Back Street Boys ya kuma taba fitowa a wasu fina-finai masu dogon zango irinsu “House of Carters.”
Tuni dai abokan aiki, da masoyansa suka yi ta aikewa da sakon taya alhini ga iyalansa.