Ana Jimamin Mutuwar Jami'an Zabe Bakwai Da Suka Rasu a Nijar

A Jamhuriyar Nijar, an shiga jimamin mutuwar ma'aikatan zabe da suka rasa rayukansu bayan da motarsu ta taka nakiya a yankin Tillabery.

Hukumar zabe ta kasa CENI ta ba da sanarwar mutuwar jami’an nata 7 yayin da aka fara tattara sakamamon zaben shugaban kasar da aka yi a ranar Lahadi.

Lamarin ya faru ne a gundumar Dargol da ke yankin Tillabery iyaka da Burkina Faso bayan da motarsu ta taka nakiya.

Daga cibiyar tattara bayanai dake dakin taro na Palais des congres ne hukumar zabe ta kasa ta sanar da jama’a wannan mummunan al’amarin da ya faru.

Da yake magana cikin yanayin alhini mataimakin shugaban hukumar ta CENI Dr Aladoua Amada ya yi mana karin bayani nuna jimaminsa kan wannan al'amari.

Kungiyoyin cikin gida masu aikin sa ido a sha’anin zabe sun bayyana takaicinsu game da faruwar wannan hatsari da ke bukatar gudanar da bincike don tantance masu alhakin faruwarsa.

Jam’iyun kawancen adawa na CAP 20 21 wadanda suka yabawa jama’ar Nijer saboda jajircewarsu wajen ganin sun kada kuri’a a zaben na jiya sun bayyana juyayi a game da rasuwar jami’an na hukumae zabe.

Shi ma dan takarar jam’iyar PNDS mai mulki Bazoum Mohamed ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa ya na matukar bakin cikin rasuwar wadanan jami’ai 7 da ake kyautata zaton aika-aika ce da ‘yan ta’adda suka shuka bisa la’akari da yadda suka addabi wannan karkara.

Kawo yanzu hukumar ta CENI ta fara tattara sakamakon zabe inda ta fara bayarda wadanda suka shigowa a cikin daren jiya saboda haka wannan aiki zai ci gaba da gudana a cibiyar tattara bayanai da ke dakin taro na Palais des congres.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Jimamin Mutuwar Jami'an Zabe Bakwai Da Suka Rasu a Nijar