Shugaban Amurka mai jiran gado yace zai ci gaba da aiwatar da takunkumin da gwamnatin Obama ta kakabawa Rasha, sai dai ba zasu dade ba.
WASHINGTON, DC —
A wata hira da jaridar Wall Street Journal tayi dashi, da ta buga a shafinta na internet jiya jumma’a, Donald Trump yace zai kyale takumkumin a kalla zuwa wani lokaci, amma zai dage idan Rasha ta taimaka ta wajen yaki da ta’addanci da kuma taimakawa wajen cimma wadansu muradu da suke da muhimmanci ga Amurka.
Ya gayawa jaridar cewa, “idan ana kyakkyawar mu’amala da Rasha zai taimaka mana, menene zai sa a kakabawa wani takunkumi idan yana yin abinda ya kamata.”
Trump ya kara da cewa, da zarar an rantsar da shi, zai shirya ganawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. “Yace naji suna so mu gana, bani da damuwa da haka.
A halin da ake ciki kuma, wani rahoto da jaridar Washington Post ta buga yace Rasha ta gayyaci gwamnatin Trump ta halarci wani zaman tattaunawar wanzar da zaman lafiya a Syria da za a yi a Astana, babban birnin kasar Kazakhstan, ’yan kwanaki bayan rantsar da Trump. Ba a gayyaci gwamnatin Obama a zaman tattaunawar ba.