Haka kuma ana ci gaba da magangannu gameda wata kasida mai shafuna 35 dake yawo a yanzu, wacce akace tana kunshe da wasu bayanai na batanci akan wasu abubuwan assha da watakila shi Donald Trump din ya aikata a asirce, wacce kuma akace wani tsohon dan leken asirin kasa na Biritaniya dake zaune a London ne mawallafinta.
Kan haka ne jiya tarin ‘yanjaridu suka yi cincirindo a gaban opishin wata cibiya mai suna “Orbis” dake London, wacce aka akace a cikinta ne aka rubuta wanna kasidar.
An kuma an bayyana cewa wani mutum mai suna Christopher Steele, tsohon ma’aikacin Hukumar leken Assirai ta MI-6 ta Ingila, wanda ya rubuta kasidar, yanzu haka ya kwashe iyalinsa, sun bata kwata-kwata, ba’a san inda suke ba.