Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sifeto Janar Na Amurka Zai Binciki Yadda Ma'aikatar Shari'a Ta Binciki Batun Clinton


Hillary Clinton da aka zarga da yin anfani da nata email wajen gudanar da auuikan gwamnati abun da ya saba ma doka
Hillary Clinton da aka zarga da yin anfani da nata email wajen gudanar da auuikan gwamnati abun da ya saba ma doka

Yayinda wannan ke faruwa ne kuma...ake bada rahoton cewa Sufeto-Janar na Amurka ya kudurta kaddamarda wani gagarumin bincike don bin diddigin yadda ma’aikatar shara’a ta Amurka, wacce yake wa aiki, ta gudanarda nata bincike akan zargin da aka yi wa tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen AmurkaA Hilary Clinton

An zargeta da yin anfani da wasu hanyoyin da basu kamata ba wajen karba da aika sakkoninta na email, daya daga cikin batutuwa mafi zafi da aka fi cece-kucce a kansu a lokacinda ake yakin neman zabe a bara.

Musamman Sufeto-Janar din, Michael Horowitz yace yana son ya fahimci yadda shugaban Hukumar FBI, James Comey ya gudanarda binciken da ya share shekara daya yana gudanarwa akan Hillary Clinton, wacce ta rike mukamin Sakatariyar-Harkokin-Wajen-Amurka daga 2009 zuwa 2013, kuma tayi kokarinh zama shugabar Amurka mace ta farko, abin ya gagara.

Hilary dai ta dora laifin kayen da aka yi mata zabe akan shi Comey a dalilin sanarwar da ya bada ta sake bude binciken da yake a kanta, ana saura kwannaki 11 kacal a yi zaben na Amurka, abinda wasu ke ganin wannan ne yasa ta fadi zaben kuma abin ya baiwa abokin takararta Donald Trump na jam’iyyar Republican damar lashe zaben.

XS
SM
MD
LG