Hukumar kula da kasashe masu tasowa ta Amurka (USAID) na kaddamar da wani taron horas da ‘yan-jarida a kasar Nijar. Maudu’in wannan taron shine a kara jawo hankalin ‘yan-jarida, da su maida hankali wajen gudanar da aikin su batare da nuna ban-banci ba, musamman yadda zabe ke kara karatowa a kasar ta Nijar.
Malan. Kadiri Idi, na hukumar yayi fashin baki akan wannan taron. Ya bayyanar da cewar idan a kayi zabe mai kyau da inganci, kuma ‘yan-jarida suka bayyanar da rahoto yadda ya kamata batare da nuna wani son kai ba, to za’a ga cewar sunyi aikin su yadda ya kamata. Kuma idan su kayi aikin su yadda ya kamata to al’uma zasu zauna lafiya, tunda labarai da suke badawa shine mafi akasarin mutane suke dogaro da shi.
Don haka ana kara jawo hankalin ‘yan-jarida na cikin gida da waje, a dai-dai lokaci mai matukar muhimanci, da su yi kokari wajen bayyanar da labarai masu asali da tushe, kuma su guji bayyanar da wani labari da zai iya harzuka mutane. Kana kada su bari ‘yan-siyasa suyi amfani da su wajen bayyanar da wani labari dake da bangaranci. Kana ‘yan-jarida su sani cewar suma suna taka muhimiyar rawa wajen ganin anyi zabe mai nagarta, musamman idan suka ga anyi wani abu wanda bai dace ba sai suyi aikin su na bayyanar da shi bisa gaskiya.
Your browser doesn’t support HTML5