Bayan kebe cibiyoyin gudanar da aikin rigakafin a ciki da wajen birnin Kano, an kaddamar da shirin yin allurar ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a ranar alhamis da ta gabata.
Wasu daga cikin wadanda ke rukunin farko da aka yi musu allurar rigakafin korona a Kano sun ce allurar babu wani alamun zafi ko radadi kuma babu wani canjin yanayi da suka jikin su. Sannan sun yi kira ga jama’a da su je a yi musu wannan allurar domin a samu nasara wajan dakile kawar da cutar.
Babbar Jami’ar dake jagorantar aikin rigakafin a cibiyar asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, Madam Nafisatu Adamu, ta ce da farko da suka fara kamar mutane ba za su fito ba amma bayan kwanaki biyar da fara aiki allurar rigakafin jama’a da ma’aikata suna fitowa.
Ta ce da farko yadda aka tsara shi ne mutum zai fara yin rijista ta yanar gizo da wayarsa idan mutum ya yi sai a tura masa lambarsa da za su shigar da ita, idan mutum bai yi ba kuma idan yaje cibiyar da ake yin wannan allurar zaka samu jami’ai a cibiyar da za su yi maka rijista nan take kuma su yi maka allurar cikin minti biyar zuwa goma.
Da take magana kan kayan aiki ta ce sun yi tanadi dukkan kayyakin aikin da ya kamata kamar kayan aikin bada taimakon gaggawa ko da mutum zai shiga wani hali an bada kayan da za’a yi masa taimako na gaggawa.
Kuma zuwa yanzu sun yiwa mutum dari da saba’in da biyar allurar rigakafin, wanda a kullum suna sa ran su yiwa mutum dari da ashirin.
Yanzu haka dai masana kiwon lafiya na bayyana yadda sinadarin allurar rigakafin cutar ta korona ke aiki a jikin bil’adama.
A hirarsa da VOA kwararre kuma masanin kiwon lafiyar al’umma a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, Dr. Auwalu Umar Gajida, lokacin da yake bayyana yadda sinadarin allurar rigakafin cutar korona ya ke aiki a jikin bil’adama ya ce kamar yadda ko wane rigakafi ya ke an fi samar da su ne ta amfani burbushin kwayar cutar, wanda idan aka sawa mutum a jikinsa sai jikinsa ya taso ya gano cewa ga wani abu ya shigo abokin gaba.
Sannan ya kara da cewa yayin da jikin ya gano haka sai ya fara samar da wasu sinadarai na garkuwar jiki, wanda su wannan garkuwar jikin sai su fara shirin yakar cutar kuma amfanin su shi ne ko da cutar ta taso sai ta kama yakinta ta tumurmushe ta.
Ko da yake rukunin farko na wadanda za’a yiwa allurar a Kano bai wuce dubu dari biyu da tara ba, gwamnatin jihar na hasashen samar da ita ga mutane miliyan 12 daga nan zuwa badi.
A lokacin da ya ke wa VOA karin bayani Dr. Tijjani Hussaini ya ce suna da mutane kusan miliyan sha biyar a jihar kuma suna sa ran za su yiwa mutum miliyan sha daya zuwa sha biyu allurar rigakafin a tsakani wannan shekara ta 2021 zuwa 2022.
Ya zuwa yanzu dai jihar Kano tana da adadin wadanda suka harbu da cutar korona sama da 3,880 kana wadanda suka mutu 109 tun lokacin da annobar ta barke a farkon shekara ta 2021.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5