Ana Fama Da Matsanancin Zafi A Amurka

Yara suna sanyaya jiki domin matsanancin zafi

Miliyoyin Amurkawa sun sake fuskantar yanayin zafi mai tsanani a jiya Lahadi a fadin kasar, yayin da mummunar ambaliyar ruwa ta mamaye sassan yamma maso tsakiyar Amurka, ciki har da wani gari a jihar Iowa wanda shima ya cika da ruwa.

Kama daga yankin mid-Atlantic zuwa Maine, da fadin yankin tafkunan Amurka da ake kira Great Lakes, da kuma yankin

Yammacin kasar zuwa California, jami'an gwamnati sun fitar da sanarwar gargadi ga mazauna wuraren akan hadarin dake tattare da tsananin zafi.

Wadansu mutane kwance kan ziyawa a bakin rafi sabili da zafi a birnin New York

A Oklahoma, ma'aunin zafi ya kai kusan 41 a ma'aunin celcius a jiya Lahadi.

A yankin yamma maso tsakiya kuma, inda jihohin South Dakota, Iowa da Minnesota suka hadu, an sami ambaliyar ruwa a karshen mako. Sannan a arewa maso yammacin Iowa, koguna 13 sun cika har sun mamaye yankin, a cewar Eric Tigges na hukumar ayyukan gaggawa a karamar hukumar Clay.

Wani yana shan ruwa sabili da zafi

An kuma tada mazauna wani gari, sannan an sanya dokar takaita fita a garin Spencer a jiya Lahadi, dare na biyu kenan a jere bayan ambaliyar da ta auku wadda ba a ga irinta ba tun shekarar 1953.

A shekarar da ta gabata Amurka ta fuskanci zafi mafi muni tun 1936, in ji masana. Wani bincike da kafanin Dillancin Labari na AP ya gudanar ya nuni da cewa, bayanai daga Cibiyar Kula da Cututtuka ta Amurka sun nuna, matsanancin zafi ya yi sanadin mutuwar fiye da 2,300, adadi mafi girma a cikin shekaru 45.

Ku Duba Wannan Ma LAFIYA UWAR JIKI: Batun Cutar Da Tsananin Zafi Ke Haddasawa Da Hanyoyin Daukar Matakan Kariya - Yuni 6, 2024