Ana Cin Zarafin Yara Shida Cikin 10 a Najeriya - UNICEF

Wasu kananan Yara a Najeriya

An gudanar da taro tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyoyin masu fafutukar kare hakkin yara daga kasashen waje da sauran masu ruwa da tsaki akan batun cin zarafin yara da a halin yanzu ya ke nema ya zama ruwan dare a Najeriyar.

Wani bincike da Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya yi, ya gano cewa ana cin zarafin kananan yara shida cikin 10 a Najeriya.

Binciken har ila yau ya nuna cewa ana kuma muzgunawa kashi 50 cikin 100 na kananan yara a kasar.

Hakan ya sa masu ruwa da tsaki suka ga ya dace a yi wani zama na musamman domin nemo bakin zaren warware wannan matsala.

“Tarihi ya nuna cewa Najeriya ta himmatu wajen tabbatar da hakkin yara, abinda mu ke so mu gani shi ne a samar da dokokin kare su a kuma aiwatar da su.” In ji Fatima Muhammed, jami’a a hukumar ta UNICEF a zantawarta da wakiliyarmu Medina Dauda a gefen taron.

Ta kara da cewa, jihohin da suka fi himmatuwa wajen kare hakkokin yara a Najeriya su ne Katsina da Yobe da kuma Kaduna, inda ta ce akwai bukatar a kara masu kwarin gwiwa.

“Akan wannan harka ta fyade da ake yi na yara da na mata, shi ma kanshi mukaddashin shugaban kasa ya kafa wani kwamiti mai dauke da,” fannonin masu ruwa da tsaki a wannan harka, “saboda a san yadda za a fita daga wannan lamari.” A cewar mai bai wa shugaban kasa shawara kan muradun karni masu dorewa, Hadiza Aminu Dorayi.

Taron har ila yau ya samu halartar sarakunan gargajiya wadanda su ma suka yi tsokaci kan dalilan da ke haddasa wannan matsala.

“Wanna duk rashin tarbiya ce ta ke kawo haka, in da akwai tarbiya ai babu wanda zai yi wannan fyade, kuma kai da ka yi fyaden, ba ka san darajar kanka ba, ballantana ka san darajar wani.” In ji Mai martaba Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Suleman, Mai Badde.

Saurari cikakkaen rahoton Medina Dauda kan wannan taro da aka yi a Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Cin Zarafin Yara Shida Cikin 10 a Najeriya - UNICEF - 3'01"