Shugaban na sojojin yayi wadannan kalaman ne a cikin jawabinsa na bude taron karawa juna sani a kan dabarun yaki na shekara shekara mai taken “Nigerian Army Combat Support”, inda yace an bullo da wannan shirin bada horon ne domin sanin makamar aiki wajen yaki da yan ta’addan Boko Haram da masu garkuwa da mutane da masu fasa bututun mai da yan bindigan Fulani makiyaya.
Tun da farko da ya bude taron, gwamnan jihar Adamawa Sen. Muhammadu Bindo Jibrilla ya yabawa dakarun Najeriya bisa nasara da suke samu a yanzu wurin fatattakar yan Boko Haram.
Shima Birgediya Janar Sani Kuka Sheka dake zama kakakin sojar kasar ya bayyana muhimmancin wannan taro da sojojin suka gudanar a birnin Yola inda yace za a ci gaba da horar da sojojin domin samun kwarewa.
Facebook Forum