Ana Cigaba da Yiwa Shugaba Buhari Addu'a

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Yayinda shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kara tsawaita hutunsa da yanzu ya keyi a London karo na biyu domin cigaba da jinya, a Najeriya kuma an dukufa da yi masa addu'ar Allah Ya Bashi lafiya domin ya samu ya cigaba da aikinsa na shugabancin kasa.

Kama daga 'yan siyasa zuwa shugabannin addini na kara nuna mahimmancin yin addu'a ga shugaban Najeriya Muhammad Buhari wanda yanzu ya shafe wata daya a London inda ake duba lafiyarsa.

A hedkwatar jam'iyyarsa ta APC mai mulki a kowane ofishi labarin shugaban ake yi da fatan Allah Ya dawo dashi Abuja domin cigaba da shugabancin kasar.

Taron kwamitin rikon kwarya na APC a jihar Gombe a karkashin kwamishanan kasafin kudi na Jihar Yobe Idi Barde Kubana taron ya fara ne da addu'a wa Shugaba Buhari tare da rufewa da yi masa addu'a wadda Sanata Danjuma Goje ya gabatar.

Sani Umar Barade na daga cikin wadanda suke ganin babban aikin da shugaban ya gudanar. Bayan yayi fatan Allah Ya Bashi lafiya Ya kuma dawo dashi lafiya yace su 'yan arewa maso gabas ko bai yi masu titi daya ba zaman lafiya da ya samar masu ya isa. Yanzu musulmai da kiristoci na iya zuwa wuraren ibadansu ba tare da jin tsoron komi ba. Yace lokacin da suke cikin rikici ko salla ba'a iya yi. Babu inda zaka je cikin kwanciyar hankali a lokacin, inji shi.

Shi ma kwamishana Idi Kubana ya kira a mance da kananan banbance banbance a yi hakuri a baiwa Shugaba Buhari goyon baya da goyon bayan jam'iyyar APC domin jawo sauran jihohin da basa cikinta su shigo su ma a yi tafiya tare dasu.

Umar Waziri Kumo mai taimakawa shugaban shawara kan lamuran siyasa a ofishin sakataren gwamnatin tarayya na alwashin farin jinin shugaban na nan kamar shekarar 2015.

Malaman Islama irin su Sheikh Abdullahi Bala Lau sun kira a kara dagewa kan addu'a.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Cigaba da Yiwa Shugaba Buhari Addu'a - 2' 43"