Ganin irin bajintar da mafarauta su ka nuna wajen fatattakar ‘yan Boko Haram daga garuruwan Mubi da Maiha da kuma cigaba da kare sassan jihar da su ke yi. Wasu ‘yan jihar da dama da aka sakaya sunayensu sun yi ta kiraye kirayen a taimaki mafarauta da sauran ‘yan banga ko ‘yan tauri da makamai kamar yadda doka ta amince.
A nasu bangaren kuwa, mafarauta da ‘yan taurin sun ce su kam babu gudu babu ja da baya. Sakataren kungiyar maharba ta jihar Adamawa, Mr. Philip James ya ce sun riga sun sadaukar da rayukansu abin da su ke bukata kawai shi ne addu’a. Shi ma Mr. Yummaris, wanda wani jigo ne a hadakar kungiyar ta maharba, ya yi kiran da gwamnoni da attajiran arewa su ma su ba da irin tasu gudunmowar. To amma ya ce Allah na bayansu. Bugu da kari, wata mace a kungiyar ta ce ita so ma ta ke ta yi arangama da mayakan sa kan. Ta ce ita ba ta jin tsoronsu.
A halin da ake ciki kuma kakakin gwamnan jihar Adamawa, Mr. P.P. Elisha ya ce maharba da ‘yan tauri na taka muhimmiyar rawa a yaki da Boko Haram saboda sun fi sojojin da ke zuwa daga nesa sanin yanayin kasar.
Your browser doesn’t support HTML5