Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya da hukumar kula da masu gudun hijira ta duniya, sun dawo da masu fafutukar haurawa kasashen turai ta hanyar da ba ta dace ba daga kasar Libya.
An sauke mutanen da su ka hada da maza 63 mata 53 a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagos.
Akwai da dama daga mutanen wadanda su ka dade a tsare a hannun jami’an shige da fice na Libya kafin ba da dama a dawo da su Najeriya.
Shugaban hukumar agajin gaggawa na yankin kudu Segun Afolayan, ya bukaci duk masu niyyar kaura zuwa wasu kasashe su rika bin ka’ida, kuma tuni gwamnatin Najeriya da hadin gwiwar hukumar kula da masu son kaura ta duniya, sun bude cibiya don kula da bukatun masu son hijira zuwa wasu kasashe.
Afolayan, ya ce akwai cibiyoyin ama’aikatar kwadago da aikin yi a Lagos, Benin da Abuja.
Nan wata ‘yar jihar Edo ke magana da gidan talabijin na Channels bayan kubutowa daga Libya, ta na shawartar mutane kar su je kasar da zai yana su da masu mugunta don ma ba sa daukar masu hijirar a matsayin mutane don su na ajiye su ne a ajin dabbobi.
Sai wani matashi daga jihar Edo shima ya na cewa kwale-kwalen su mai inji ya ci kilomita 5 a cikin tekun Bahar Rum don neman ketarawa turai, sai injin ya mutu don haka su ka yi ta ninkaya har a ka zo a ka cece su, amma wani kwale-kwalen kuma a ranar ya kife ne duk mutanen ciki sun mutu.
‘Yan Najeriya dai kan samu kan su a tsaka mai wuya in sun shiga turai ba bisa ka’ida ba, don mata kan iya aukawa karuwanci maza kuma su biyewa harkar miyagun kwayoyi.
Jami’in hukumar yaki da fatauncin miyagun kwayoyi Hamisu Lawal, ya ce sun dage don dakile hana fitar masu fataucin don kare mutuncin Najeriya.
Hakika kyautatawa ‘yan kasa da aiyukan yi da aiwatar da dokokin hana balaguro ba bisa ka’ida ba za su rage wannan kalubale, da kan maida ‘yan Najeriya masu ficewa ta barauniyar hanya kamar bayi a zamanin mulkin mallaka.
Your browser doesn’t support HTML5