Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yara Da Dama Suna Shakar Gurbatacciyar Iska Kowacce Rana


BORNO: Sabbin marayu 'yan makaranta
BORNO: Sabbin marayu 'yan makaranta

Hukumar kula da lafiya ta duniya wato WHO ta sanar cewa fiye da kashi casa’in cikin dari na yara yan kasa da shekara goma sha biyar a fadin duniya suke shekar iska mai dauke da guba a kowacce rana yanayin dake jefa lafiyarsu cikin mummunar hatsari.

Hukumar kula da lafiya ta duniya ta fitar da wannan bayani ne a taron data gudanar a Geneva a karshen watan oktoban wannan shekarar.

Hukumar kula da lafiyar tace a shekarar 2016 yara dubu dari shida ne suka mutu sanadiyar cututtukar da ake dauka ta hanyar shakar gurbatacciyar iska , bugu da kari wani sabon rahoton hukumar lafiyar kan gurbatacciyar iska da kuma lafiyar yara ya lura cewa gurbatacciyar iskar tafi samuwa ne a tsakankanin gidaje da kuma wajen gidajen kasashen marasa abun hannu da kuma matsakaita. Binciken har ila yau yace muddin mace mai juna biyu ta kasance cikin yanayin gurbatacciyar iska, akwai yiwuwar ta haifi jaririn da bai kosa ba.

Wani dalili kuma da yasa yara suka fi fuskantar barazanar gurbatacciyar iska shine garkuwan jikinsu ba kamar na manya bane

Daga matakan daza a dauka don rage barazanar da gurbatacciyar iska ke yi wa lafiyar yara, akwai samar da makarantu da filayen wasanni masu tazara daga manyan ababen da suke haifar da gurbacewar iska da suka hada da tituna da ake hada hadar ababan hawa, masana’antu da kuma tashoshin samar da makamashi.

Saurari Cikakken rahoton Abdulwahab Mohammed:

Kananan yara na shakar iska mai guba-3:42"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG