Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Italiya Tana Daukar Matakan Maido Da Zaman Lafiya A Kasar Libya


Fara Ministan Italiya Giuseppe Conte
Fara Ministan Italiya Giuseppe Conte

Kasar Italiya ta shirya wani taron koli na kwanaki biyu a kan kasar Libya, tana mai fatan samar da zaman lafiya da zaben dimokaradiyya ga kasar dake fama da tashe-tashen hankula.

Jiya Linitin Fara ministan Italiya, Giuseppe Conte, ya ce manufarsu itace “su taimaka wajen kawo karshen yakin da ake a Libya da kuma daura kasar kan tafarkin zaman lafiya… ya ci gaba da cewa muna son ‘yan kasar Libya su sami damar zaben abin da suke so.”

Kasar Italiya dai tana da manufa ta musamman akan abubuwan da suke gudana a Libya.

Kasancewar Italiya itace kasa ta farko da bakin haure ke fara zuwa, akan hanyarsu ta shiga Turai daga gabar tekun Libya. Yawancin lokuta kuma masu safarar mutane kan bar jiragensu da suka lalace a tekun Meditaraniya mai hatsarin gaske.

Bayan kwashe shekaru suna neman taimakon kungiyar tarayyar Turai da sauran kasashe, yanzu haka dai gwamnatin Italiya ta rufe tashoshinta ta ga jiragen bakin haure, tana mai tilasta musu su nemi wani wajen sauka bayan kwashe makonni a ruwa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG