Ana Cia Gaba Da Sa-In-Sa A Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya

Wasu Bayanai na nuni da cewar wata baraka ta taso a hukumar dake kula da wasan kwallon Kafa ta tarayyar Najeriya NFF tsakanin Mr Chris Giwa, da shugaban hukumar Amaju Pinnick.

Bayan dawowar hukumar kwallon kafa ta Najeriya daga gasar cin kofin duniya da akeyi a Rasha, 2018, NFF ta samu wata sanarwa da ta gaggauta gabatar da Chris Giwa a matsayin halartaccen shugaban hukumar a maimakon Amaju Pinnick, wanda shi ne babban shugaban hukumar NFF.

Wata jarida a Najeriya ta wallafa cewa Mr Giwa, tare da wasu 'yan majalisarsa, sun isa ofisoshin NFF kimanin 12:00 na yamma a ranar litinin don aiwatar da hukuncin Kotun Koli, wanda ta karyata zaben Mr. Pinnick a matsayin shugaba ta kuma umurci Giwa sa matsayin halartaccen shugaba hukumar.

Amma a cikin gaggawa, Mr Pinnick, ya ci gaba da cewa har yanzu shine shugaba a Hukumar NFF, Jaridar Vanguards, ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewar Ministan matasa da wasanni Solomon Dalung ya bukaci hukumar da ta tabbatar da Mr Giwa a matsayin shugaban hukumar NFF, kamar yadda kotu ta umurta.

Da yake magana da lauya mai kula da hukumar ta NFF, Mr. Festus Keyamo, Pinnick yayi ikirarin cewa kotu ba ta da alaka da NFF.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Cia Gaba Da Sa-In-Sa A Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya