Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Andres Iniesta Ya Aje Takalma


Dan wasan tsakiya na kasar Spain, Andres Iniesta, wanda ya zura kwallon da ta ba Spain, damar lashe gasar kofin kwallon Kafa ta duniya a shekarar 2010, ya ajiye takalman buga wasa a kasarsa ta haihuwa Spain, bayan an fitar da su daga gasar cin kofin duniya da ake yi yanzu haka a Rasha 2018.

Dan kwallon mai shekaru 34 da haihuwa an sako shi ne bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a wasan da Spain ta sha kashi a hannun Rasha da ci 4-3 a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka shafe mintuna 120 ana 1-1 a zagaye na 16 ranar Lahadi a gasar ta bana.

Kwallon karshe da Iniesta, ya buga ita ce bugun daga kai sai mai tsaron gida da ya ci a wasan wanda shi ne wasansa na 131 da ya buga wa kasar ta Spain. Bayan tashi daga wasan Dan wasan ya ce "wannan shi ne wasana na karshe a tawagar," a cewarsa.

Iniesta, wanda ya fara bugawa kasar kwallo a 2006, ya kuma samu nasarar lashe gasar kasashen Turai a shekara ta 2008 da 2012. Iniesta ya ce Wani lokacin ba ka samun kyakkyawan karshe kamar yadda ka bukata, wannan ita ce ranar da ta fi kowacce muni a rayuwata.

A watan Mayu 2018 ne Iniesta, ya kawo karshen shekara 22 da ya shafe a kungiyar kwallon Kafa ta Barcelona, ta kasar ta Spain inda ya koma kulob din Vissel Kobe na kasar Japan. Ya lashe kofuna 32 a Barcelona, inda ya buga wa babbar tawagar kungiyar wasanni har 674 bayan da ya fara a karamar tawagar tun yana dan shekara 12 a duniya.

Kocin tawagar kasar Spain Fernando Hierro, ya bayyana Iniesta a matsayin babban dan wasa wanda ya sadaukar da Kansa ga kasarsa a bangaren wasan kwallon Kafa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG