A cikin sa'o'i 24 bayan da Super Eagles ta fice daga gasar cin kofin duniya ta 2018 a Rasha, kungiyar 'mafia' a cikin kwallon kafa tuni suka fara yakin neman zabe don kawo karshen mulkin Amaju Pinnick a hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF.
Ko da kafin NFF ta fara tafiya zuwa Rasha, wasu mambobin kwamitin da ma'aikatan sakatariyar sun gaza tafiya tare da Pinnick saboda abin da suka kira da 'girman kai' da kuma son zuciya.'' da Suna jira ne kawai su fita daga gasar cin kofin duniya kafin su fito da launi mai kyau, "in ji wani babban jami'in hukumar kwallon kafa ta NFF a hirar sa da jaridar Guardian a St Petersburg, inda aka doke Super Eagles, a gasar cin kofin duniya na bana tsakaninta da Argentina.
Ya kuma bayyana cewa Amaju Pinnick, jagora ne da bai iya gudanar da mulki a daidai ba, y ace yafi so ya aiwatar da komai shi kadai bayan haka kuma ya haifar da babban bambanci tsakanin kowane ma'aikacin a NFF.
Ya kara da cewa “Mun kasance muna shan wuya a amman munyi shiru, Saboda haka yanzu ya ƙare nasa dole ne ya tafi, "
In ji shi, a cikin laifuffukan da ya aikata, mutane sun zargi Pinnick da kawo wasu tawagar NFF kasar Rasha wadanda basu da wani aikinyi a gasar cin kofin duniya.
Wani abun kunya shine yadda aka wulakanta wasu jami'an hukumar a hotel dinsu saboda rashin kammala kudin hotel da bai yiba sakamakon ya debo wasu mutanen da basu da alaka da gasar.
A watan satumba ne dai hukumar ta NFF zata gudanar da sabon Zabe na shugabannin hukumar bayanda Amaju Pinnick da jami'ansu wa'adinsu ya kare.
Facebook Forum