Za a iya cewa a Najeriyar tun tsakiyar damunar bara a ke ganin man fetur din na tashin gauron zabi da karanci a kasuwannin kasar.
A yanzu a na ganin kasashen da suka ci gaba wajen kafuwar tattalin arziki da kimiyya sun fara ajiye man fetur a matsayin wani babban jigo da ke tallafawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasa.
Har yanzu a Najeriya kasar ta dogara ne da man fetur duk da cewa kasa ce da ke da dimbin arzikin ma’adanai da kasar noma.
Mutane kan shafe sa’o’i a kan layi a gidajen mai wanda hakan ke kawo matsala ko cikas a sana’o’i har ma da lamuran su na yau da kullum.
Wasu mazauna babban birnin kasar Abuja sun koka kan karancin man da kuma tsadar rayuwa, inda suka ce yanzu kudin mota ya karu don haka sun rage yin tafiye tafiye.
Baya ga karancin man wani abun dubawa kuma shi ne yadda farashinsa ya bambanta a jihohi, da hakan zai iya kawo ta’azzarar talauci a wasu bangarorin kasar.
Isa Abdullahi, wani mai sharhi kan harkokin tattalin arzikin kasa, ya ce sai gwamnati ta tsaya tsayin daka don gyara yadda ake tafi da harkar man fetur a kasar.
Duk da cewa a koda yaushe gwamnatin kasar da manyan dillalan man na bayyana dalilan tashin farashin man amma a wannan karon dalilin ya sha bambam da wanda aka saba ji baya.
Anasa bangaren, jagoran kungiyar dillalen man fetur wato IPMAN, Abubakar Maigandi Dakingari, ya ce wannan dogayen layuka da aka gani na da nasaba da zaben da aka yi na shugaban kasa, inda mafi yawancin direbobi ba su je wajen yin lodi ba, suna tunanin cew za a samun rashin zaman lafiya.
Ya ce a halin da ake cikin yanzu sun umarci dukkan direbobinsu da su je su yo lodi su dawo da wadannan kaya domin a fara saida wa jama’a, kuma yanzu an fara samun saukin dogayen layuka a gidajen mai a Abuja.
Ana sa ran samun saukin lamarin bayan kammala zaben gwamnoni da za a yi a ranar Asabar din nan mai zuwa.
Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar:
Your browser doesn’t support HTML5