An dai kafa kwamitocin ne don nemo bakin zaren gyara ayyukan ‘yan sanda a Najeriya. Yayin da wadannan kwamitoci ke samun korafe-korafe daga kungiyoyi da kuma daidaikun jama'a, tuni aka soma samun bahasi na irin cin zarafin da ake zargin wasu ‘yan sanda na yi, da sunan gudanar da aiki, ciki har da kisa tun kafin yanke hukunci ko kuma azabtarwa don tatsar bayanai daga wadanda aka kama ko ake zargi da sunan laifi.
A zaman kwamitin a jihar Adamawa, an kai ruwa rana tsakanin lauyan ‘yan sanda da wasu da suka shigar da korafi wanda hakan ya sa shugaban kwamitin a jihar kuma tsohon alkali, Justice Adamu Hobon yin kira ga bangaren ‘yan sanda da su daina jan kafa.
Cikin wadanda suka shigar da kara gaban kwamitin har da iyayen wani matashi Mr. Kane Nicks Kaino, da suke zargin ‘yan sanda da kashe shi ba tare da hukuncin Kotu ba.
Barr Leonard Zidon, da ke jagorantar lauyoyin matashin ya ce suna bukatar a yi bincike da kuma biyan diya idan da bukatar yin hakan.
To ko wacce damara rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta yi domin kare kanta yayin da wasu batutuwa suka fara fitowa? DSP Bamanga Abana, shi ne jami'in kula da harkokin Sharia na rundunar ‘yan sandan jihar, ya ce duk wani bahasi da kwamitin ya ke bukata zasu bayar da shi.
Yanzu dai lokaci ne kawai ke iya tabbatar da danbarwar da zata kaya a gaban irin wadannan kwamitocin jin bahasin da kuma ko shin rahoton kwamitocin zai yi aiki ko kuma a'a.
Saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul'aziz.
Your browser doesn’t support HTML5