Taron dai dalinin abin da ke kara fayyace girman barakar da ke tsakanin kusoshin jam’iyar, sakamakon rikicin shugabancin da ya barke a tsakaninsu, duk da cewa kowanne daga cikin bangarorin na jaddada goyon baya ga takarar Hama Amadou a zaben 2021.
A zauren Palais du 29 Juillet da ke birnin Yamai ne a jiya Lahadi da daddare lokacin da magoya bayan jam’iyyar Moden Lumana ke fayyace mahimman shawarwarin da suka tsayar bayan tattaunawar wuni daya karon farko.
A daya bangare wasu magoya bayan jam’iyyar ta adawa sun shirya makamancin wannan taro a jiyan a garin Dosso a karkashin jagorancin mutumin da kotu ta bayyana a matsayin halartaccen shugaban riko, wato Oumarou Noma, wanda a karshen taro ya bayyana matsayinsa game da halin da ake ciki a yau a Moden Lumana.
A sakon bidiyon da ya aikawa mahalarta taron na Birnin Yamai, Hama Amadou da ke gudun hijira a Jamhuriyar Benin, ya gargadi bangarori da su yafewa juna domin ci gaban jam’iyyar.
Sabanin yadda shugabanni ke ja-ni-in-jaka, magoya bayan jam’iyyar ta Lumana Afirka, sun yi na'am kan bukatar a hada kai don dora Hama Amadou akan kujerar shugabancin kasa a 2021.
Yanzu dai kallo ya koma ma’aikatar cikin gida wacce dokokin Jamhuriyar Nijar suka dorawa alhakin tantance halaccin shawarwarin karshen taron jam’iyyun siyasa, ko da yake, doka ta ba da damar garzayawa kotu ga duk wanda ke ganin ba a yi masa adalci ba.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5