Ranar Lahadi 6 ga watan Disamba da maraice ne tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulazeez Yari ya yi hira da manema labarai inda ya yi korafi akan zaben da aka ce bai kammalu ba. Ya kuma zargi jam'iyyar PDP da saye kuri'un masu zabe da kuma yin amfani da jami'an tsaro wajen yi wa jama'a barazana. Bayan haka ya ce za su bi duk wata hanya da ta dace ta shari'a don kare muradansu.
Shi kuma shugaban jam'iyyar PDP na jihar Zamfara, ya musanta duk zarge-zargen da tsohon gwamnan ya yi, ya kuma caccaki gwamnatinsa ta APC da cewa ba ta yi wa al'umar jihar komai ba tsawon shekara 8.
Ya kara da cewa jam'iyyar APC ta dauko masu tada zaune tsaye don ganin sun ci zabe karfi da yaji, ya kuma bayyana cewa su na da kwakkwarar shaida akan duk kulle-kullen da tsohon gwamnan yayi don neman cin zabe.
Hakan na faruwa ne bayan da a ranar Alhamis 3 ga watan Disamba, jam'iyyar PDP mai mulki a jihar ta yi korafin cewa an kashe mata wasu magoya bayanta yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben cike gurbi na dan majalisar dokin jihar a karamar hukumar Bakura.
Saurari cikakken rahoton Sani Shu'aibu Malumfashi:
Your browser doesn’t support HTML5