A farkon shekarar nan babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yankewa Maryam hukuncin kisa bayan da ta same ta da laifin kashe mijinta Bilyaminu Bello, da ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP a Najeriya.
Alkalan kotun uku da suka yanke hukuncin a ranar Juma'a, sun ce hujjojin da Maryam ta gabatar na kare kanta ba su da tushe balle makama, abin da suka ce ya zama dole a yi adalci.
Hujjoji da bayanai da aka gabatar a gaban kotun sun nuna cewa Maryam ce ta yi ajalin mijinta a shekarar 2017 ta hanyar caka masa wuka bayan da ma'auratan biyu suka samu sabani.
Ita dai Maryam wacce take da ‘ya’ya biyu da marigayin, ta ce Bilyaminu ya fada ne akan tukunyar shisha lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito lauyoyin Maryam suna cewa za su daukaka kara zuwa kotun kolin kasar.