Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bauchi Na Cikin Jahohin Da Ke Da Muhallai Mafiya Kyau a Najeriya - Inji Kwararru


Gwamnan Bauchi Bala Mohammed (Kauran Bauchi).
Gwamnan Bauchi Bala Mohammed (Kauran Bauchi).

Bayan zagaya jahohin Najeriya, kwararru da su ka hada da na ciki da wajen Najeriya, sun ce jahar Bauchi ta matukar burge su saboda tsaftarta.

Tawagar kwararru su goma sha biyar dake nazarin muhalli karkashin jagorancin Farfesa Solomon Balogun, masani a Jami’ar Wisconsin, Madison ta kasar Amurka sun bayyana cewa yanayin muhallin jihar Bauchi na daya daga cikin mafiya kyau a Najeriya, wanda zai zama abin koyi a duk fadin kasar.

Wannan yabo an yi shi ne a wajen bikin kaddamar Cibiyar Gudanar da Binciken Ruwa da Iska da Tsire-tsire da Abinci.

Filin Wasan Jihar Bauchi
Filin Wasan Jihar Bauchi

Taron kaddamar da cibiyar Binciken ya samu halartar masana yanayin muhalli da kuma kungiyoyin masu rajin kare muhalli a ciki da kuma wajen jihar Bauchi. Mallam Samaila Bima, shi ne shugaban kungiyar Jewel Enviromental Iniative a Najeriya kuma ya yi tsokaci kan yadda yanayin Muhalli yake a shiyyar arewa maso gabas da kuma dalilan da yake kai ga jiha ta zamo mai tsafta, wanda wadannan dalilan su ka sa Bauchi ta zama mai tsafta.

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Kauran Bauchi, shi ma an karrama shi sabili da wannan fice da ya yi kan batun tsaftar muhalli, ya ce wannan karramawar na al’ummar jihar Bauchi, ta fara ne da bayyana matsayin yadda tsaftar muhalli ta ke kafin hawansa kujerar Mulki.

Domin sanin yadda na’urar kimiyyar binciken yanayi ke aiki wakilin Muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad ya nemi bayani daga bakin Darakta Janar na hukumar kare muhalli a jihar Bauchi, Dakta Ibrahim Umar, wanda ya yi bayani dalla dalla.

Ga Abdulwahab Muhammad da ciakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG